Adadin mutanen da suka mutu sakamakon mummunar ambaliyar ruwa a babban birnin Ghana, Accra, ya kai aƙalla 12, yayin da jami’an agaji ke gargaɗin cewa adadin na iya ƙaruwa saboda har yanzu akan aikin ceto.
Ƙungiyoyin ceto sun ceci sama da mutane 400 bayan ruwan sama mai ƙarfi ya mamaye gidaje da hanyoyi a fadin birnin.
Gwamnati ta ba da haƙuri kan yadda ta tunkari lamarin, yayin da Shugaba John Mahama ya fitar da kuɗaɗen gaggawa tare da tura sojoji da ’yan sanda domin taimakawa ayyukan agaji.
- Tehran ta musanta shirin tattaunawa da Amurka da Trump yace za a yi
- Shugaban adawar jamhuriyar dimokuraɗiyar congo ya ce an hana shi fita daga ƙasar
- HRW: Bangarorin da ke yaƙi a Mali na cin zarafin Bil Adama
Hukumomi sun yi gargadin cewa duk da ruwan ya ragu, ƙasar da ta jike sosai na nufin har yanzu akwai babban haɗarin sake samun ambaliya.