Ɗaya daga cikin manyan jagororin adawa a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo (DR Congo), Delly Sesanga, ya ce jami’an gwamnati sun hana shi barin ƙasar tare da ƙwace fasfo ɗinsa, lamarin da ya bayyana a matsayin wani yunkuri na tsoratarwa da kuma takura masa.

Sesanga, shugaban jam’iyyar Envol, tsohon minista kuma tsohon ɗan majalisa, na daga cikin jagororin sabuwar ƙungiyar adawa da ke ƙin shirin gwamnatin Shugaba Félix Tshisekedi na sauya kundin tsarin mulki.

A farkon watan nan ne majalisar dokokin ƙasar ta amince da kudirin dokar gudanar da ƙuri’ar raba gardama kan gyaran kundin tsarin mulki, masu adawa na zargin cewa wannan mataki zai bai wa Shugaba  damar sake tsayawa takara karo na uku duk da cewa wa’adinsa na biyu zai ƙare a watan Disamba a shekara ta 2028, a ranar 12 ga Yuni, jami’an tsaro sun tarwatsa zanga-zangar adawa da aka gudanar a birnin Kinshasa domin nuna adawa da abin da masu zanga-zangar suka kira “yunƙurin juyin mulki ta hanyar kundin tsarin mulki.

Rikicin ya yi sanadin jirkitar da wasu shugabannin adawa ciki har da Delly Sesanga, yayin da Ofishin kwamishinan kare haƙƙoƙin  dan Adam na majalisar ɗinkin  duniya ya ce aƙalla mutum ɗaya ya rasa ransa, kuma an shirya sake gudanar da wata zanga-zanga a ranar 8 ga watan Yuli, Sesanga wanda ke cikin ƙungiyar C64 (Coalition Article 64) da aka kafa domin adawa da shirin sauya kundin tsarin mulki, ya shaida wa manema labarai cewa lokacin da ya je filin jirgin sama a ranar Lahadi domin tafiya Turai neman magani saboda raunukan da ya samu a zanga-zangar, jami’an shige da fice sun ƙwace fasfo ɗinsa tare da sanar da shi cewa ba a ba shi izinin fita daga ƙasar ba.
Ya ce an umurce shi da ya tuntuɓi hukumomin shari’a, amma ba a bayyana masa dalilin wannan mataki ba a cewarsa wannan tsoratarwa ce da kuma nuna rashin bin ka’ida, yace bai samu wata sanarwa cewa ana gudanar da bincike a kansa ba sai dai kamfanin dillancin labarai na gwamnatin Congo ya rawaito cewa wata majiya daga bangaren shari’a ta tabbatar da cewa ana gudanar da bincike kan Sesanga.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *