Kotun Ƙoli ta Amurka ta yanke hukunci a kan umarnin Shugaban Amurka Donald Trump na soke haƙƙin zama ɗan ƙasar Amurka ga duk wanda aka haifa a ƙasar.

Wannan hukunci da aka yanke da ƙuri’a 6-3 ya zama babban cikas ga Trump da ƙoƙarinsa na sauya manufofin shige da fice na Amurka.

Bayan da ya karɓi mulki a ranar 20 ga Janairu, 2025, Trump ya sanya hannu kan wani umarnin zartarwa da ke neman hana waɗanda aka haifa a Amurka ga iyayen da ke da matsayin zama na wucin gadi ko kuma ba su da takardun shari’a samun zama ɗan ƙasa kai tsaye.

Kotun Ƙoli mai mambobi tara ta tabbatar da hukuncin wata kotun ƙasa da ta riga ta ce umarnin Trump ya saɓa wa Kundin Tsarin Mulkin Amurka, tare da wani hukunci na Kotun Ƙoli da ya gabata kan wannan batu.

A cikin rubutaccen hukuncinsa mai shafuka 26, Babban Alƙali John Roberts ya bayyana cewa tsarin haƙƙin zama ɗan ƙasa ta haihuwa a Amurka ya samo asali ne daga dokokin gargajiyar Ingila, har zuwa amincewa da kwaskwarimar Kundin Tsarin Mulki na 14 a shekarar 1868, da kuma hukuncin Kotun Ƙoli na 1898 a shari’ar United States da Wong Kim Ark.

Ya ce lauyoyin gwamnatin Trump da wasu alƙalan Kotun Ƙoli da suka  ƙi yarda da hukuncin ba su gabatar da isasshiyar hujja ba wajen sabunta wannan fahimta ta doka da ta daɗe.

Roberts ya samu goyon bayan wasu alƙalan da ke da ra’ayin mazan jiya: Amy Coney Barrett da Brett Kavanaugh, tare da dukkan alƙalan da ke da ra’ayin sassaucin ra’ayi: Sonia Sotomayor da Ketanji Brown da Jackson, da Elena Kagan.

Trump, a nasa ɓangaren, ya bayyana hukuncin a matsayin “abin takaici ga ƙasarmu,” sannan ya yi kira ga ‘yan jam’iyyar Republican a Majalisa su kafa doka da za ta takaita haƙƙin zama ɗan ƙasa ta haihuwa.

Amma hakan na iya zama abu mai wahala sosai, domin binciken ra’ayoyin jama’a yana nuna cewa mutane da yawa na goyon bayan wannan tsarin, kuma hukuncin Kotun Ƙoli ya nuna cewa sai an yi kwaskwarimar Kundin Tsarin Mulki idan za a canza shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *