Gwamnatin Jihar Benue ta sanar da shirinta na kafa Cibiyoyin Koyon Ilimin Zamani na Dijital (Digital Learning Centres – DLCs) guda 13 a wasu zabaɓɓun makarantu domin inganta damar samun ilimi ta hanyar amfani da fasaha.
Shugabar Hukumar Ilimin Bai Ɗaya ta Jihar Benue (SUBEB), Grace Adagba, ce ta bayyana hakan a ranar Talata yayin taron tattaunawa na Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya da Hukumar Ilimin Bai Ɗaya ta Ƙasa (FME-UBEC) kan amfani da kayan aikin dijital a Abuja.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Hukumar taa SUBEB, Msughter Ataigbough, ya fitar, an bayyana cewa cibiyoyin za su kasance wani ɓangare na ƙoƙarin gwamnatin jihar na samar da yanayin koyo da koyarwa da ke amfani da fasaha, domin inganta koyarwa, koyo da kuma samun ingantattun kayan ilimi.
Adagba ta ce wannan shiri ya yi daidai da manufar Gwamna Hyacinth Alia ta sauya fasalin fannin ilimi ta hanyar amfani da fasahar zamani.
- Mummunar ambaliyar ruwa ta halaka mutum 12 Accra
- Zama ɗan Kasa: Hukuncin Kotun Ƙoli ya saɓawa ra’ayin Trump
- Da Ɗumi-Ɗumi: Za a fara gasar NPFL ta kakar bana a watan Augusta
Ta kuma bayyana shirye-shiryen ilimin dijital da jihar ke aiwatarwa, tare da jaddada kudirin SUBEB na rungumar sabbin fasahohin ilimi da Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya da UBEC suka gabatar.
A cewarta, kasancewarta memba a Kwamitin Ƙasa na Fasahar Ilimi (National EdTech Committee on Achieving Learning Outcomes), Jihar Benue ta shirya tsaf domin aiwatar da amfani da kayan aikin dijital da suka dace, domin ƙarfafa koyarwa da koyo a makarantun gwamnati.
Ta ƙara da cewa haɗa fasaha cikin azuzuwan karatu zai taimaka wajen bai wa ɗalibai ƙwarewar da suke buƙata domin su iya gogayya a duniyar zamani mai saurin bunƙasa ta fuskar fasahar dijital.