Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya yi kira ga ƙwararrun ma’aikatan da suka yi ritaya daga ɓangaren wutar lantarki a Najeriya da su mara wa ƙoƙarin da ake yi na gyaran tsarin samar da wutar lantarki baya.

Gwamna Ododo ya yi wannan kira ne a yayin wata ganawa da tsofaffin shugabanni da masana a fannin wutar lantarki, inda ya yaba da irin gudunmawar da suka bayar wajen bunƙasa harkar wutar lantarki a ƙasar.

Ya ce ƙwarewarsu da gogewar da suka tara tsawon shekaru na da matuƙar muhimmanci wajen magance matsalolin wutar lantarki da Najeriya ke fama da su tun shekaru masu yawa.

Gwanaan Jihar ta Kogi  ya yi tsokaci da kalaman tsohon Firaministan Birtaniya, Winston Churchill, gwamnan ya ce ci gaba mai ɗorewa yana samuwa ne idan aka koyi darasi daga waɗanda suka kafa tubalin manyan cibiyoyi.

Ododo, wanda tsohon ma’aikaci ne na tsohuwar Hukumar Wutar Lantarki ta Ƙasa (NEPA), ya bayyana taron a matsayin wata dama ta sake haɗuwa da malamansa da abokan aikinsa waɗanda suka taka muhimmiyar rawa wajen gina rayuwarsa ta sana’a.

Ya ƙara da cewa ƙa’idojin aiki kamar ladabi, haɗin kai da riƙon amana da ya koya a lokacin da yake aiki a ɓangaren wutar lantarki har yanzu suna jagorantar salon shugabancinsa.

Gwamnan ya jaddada cewa samar da ingantacciyar wutar lantarki na da matuƙar muhimmanci wajen bunƙasa masana’antu, jawo masu zuba jari, inganta harkokin lafiya da ilimi, da kuma samar da ayyukan yi.

“Ƙasa har yanzu tana buƙatar ƙwarewarku da gogewarku da shawarwarinku,” in ji gwamnan ga waɗanda suka yi ritaya.

Da yake jawabi a madadin ƙungiyar, Dr. Samuel Agbogun ya yaba da yadda gwamnan ke gudanar da mulki, musamman a fannoni na shugabanci da tsaro.

Sauran waɗanda suka yi jawabi, ciki har da Engr. Akin Bada da Engr. Hope Toru da Engr. Ibrahim Hashim, sun yi maraba da kafa Hukumar Kula da Tsarin Wutar Lantarki ta Jihar Kogi, suna masu cewa hakan zai ƙarfafa tsarin sa ido da gudanarwa, ya jawo masu zuba jari, tare da inganta samar da wutar lantarki

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *