Honarabul Lado Suleja ya yabawa Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai na Ƙasa, Alhaji Muhammad Idris Malagi, bisa abin da ya bayyana a matsayin jagoranci nagari da ƙoƙarinsa na ganin Jihar Neja na ci gaba da samun ayyukan raya ƙasa.
A cikin wata sanarwa, Lado Suleja ya ce amincewar Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) da gina kusan kilomita 409 na tituna a sassa daban-daban na Jihar Neja wani babban ci gaba ne da zai inganta sufuri, bunƙasa kasuwanci, ƙarfafa harkokin noma, da kuma tallafa wa ci gaban tattalin arziki da tsaro a jihar.
Ya ce wannan mataki na nuna ƙudirin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na aiwatar da muhimman ayyukan raya ƙasa a ƙarƙashin manufofin sabunta kása (Renewed Hope Agenda).
-
Gwamnatin tarayya ta yi wa NYSC garambawul
-
‘Yan sanda sun kama matar da ake zargi da yunkurin kashe mijinta a Jihar Katsina
Lado Suleja ya kuma yaba da rawar da Ministan Yaɗa Labarai, Alhaji Muhammad Idris Malagi, ya taka wajen tabbatar da cewa buƙatun ci gaban Jihar Neja na samun kulawa a matakin gwamnatin tarayya.
Hakazalika, ya gode wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Majalisar Zartarwa ta Tarayya da Ministan Ayyuka da sauran hukumomin da abin ya shafa bisa amincewa da ayyukan titunan.
Ya kuma yi kira ga al’ummar Jihar Neja da su ci gaba da bai wa shirye-shiryen gwamnatin tarayya goyon baya, yana mai cewa haɗin kai da haɗin gwiwa ne za su tabbatar da dorewar ci gaban ƙasa. Ya kuma yi addu’ar Allah Ya ba shugabannin ƙasar hikima da lafiya da ƙarfin guiwar ci gaba da yi wa Najeriya hidima.