Gwamnatin Tarayya ta bayyana shirinta na kawo sauyi a tsarin ilimin sakandare a Najeriya, inda za ta soke tsarin raba makarantar sakandare zuwa ƙaramar sakandare (JSS) da babbar sakandare (SSS), saboda yadda tsarin ya gaza rage yawan yaran da ke barin makaranta.

Ministan Ilimi Dakta Maruf Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan a Abuja yayin ƙaddamar da kwamitin sa ido da aiwatar da ayyukan hukumar ilimin bai ɗaya ta ƙasa  UBEC.

A cewarsa,  binciken gwamnati ya nuna cewa Najeriya na da kusan makarantun firamare dubu 80 na gwamnati, amma makarantun ƙaramar  sakandare kusan dubu 15 ne kacal.

Jaridar Blueprint ta ruwaito cewa Dr Alausa ya ce wannan giɓin ya sa miliyoyin yara ke ƙasa  ci gaba da karatu bayan sun kammala firamare.

Ministan ya ce sama da yara miliyan 24 ne ke shiga makarantar firamare a Najeriya, amma kusan miliyan hudu ne kawai ke kaiwa matakin kammala babbar sakandare, ya ce hakan na nufin fiye da yara miliyan 20 na ficewa daga tsarin karatu kafin su kai matakin kammala sakandare.

Dakta Alausa ya ce gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ƙuduri aniyar magance wannan matsala ta hanyar sauya tsarin ilimi domin bai wa yara damar ci gaba da karatu ba tare da tsaiko ba.

Ya kuma bayyana cewa za a gabatar da kudirin soke tsarin raba JSS da SSS a taron gaba na Majalisar Ilimi ta Ƙasa domin amincewa da shi.

Ministan ya ƙaddamar da wani kwamitin kwararru ƙarkashin jagorancin Farfesa Rashid Aderinoye domin hanzarta kammalawa da fara amfani da makarantun zamani da makarantun harsuna biyu  da hukumar UBEC ke ginawa a sassan ƙasar.

Sakataren zartarwa ta UBEC, Aisha Garba, ta ce an riga an gina Makarantun zamani 37 a faɗin Najeriya, inda 24 daga cikinsu suka fara aiki yayin da sauran ke kan matakin kammalawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *