Rundunar ‘yan sandan Jihar Katsina ta kama wata matar aure mai shekaru 23, bisa zargin yunkurin kashe mijinta ta hanyar sare masa wuya da wuƘa  yayin da yake barci.

Mai magana da yawun rundunar DSP Abubakar Sadiq Aliyu, ya ce lamarin ya faru ne a cikin birnin Katsina.

A  cewarsa,  mijin mai suna Jamilu Ibrahim ya kai rahoto ofishin ‘yan sanda na kasuwar tsakiya da misalin karfe tara na safe inda ya bayyana cewa matarsa, Sadiya Lawal, ta kai masa hari da misalin ƙarfe  biyar da rabi na asubahin ranar lokacin da yake barci.

Rahotanni sun ce matar ta yi koƙarin sare masa wuya da wata kaifaffiyar wuƙa  lamarin da ya janyo masa mummunan rauni a wuya.

An garzaya da Jamilu Ibrahim zuwa asibiti domin samun kulawar likitoci, kuma jami’an lafiya sun tabbatar da cewa yana ci gaba da samun sauki, bayan samun rahoton, jami’an binciken manyan laifuka sun kai ziyara wurin da lamarin ya faru inda suka kama matar tare da kwato wukar da ake zargin an yi amfani da ita wajen harin.

Rundunar ‘yan sanda ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano musabbabin faruwar lamarin yayin da matar ke ci gaba da kasancewa a tsare sai dai rundunar ta jaddada cewa zargin da ake yi wa matar bai zama hujjar laifi ba har sai kotu ta tabbatar da hakan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *