Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi,

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya buƙaci Hukumar Zaɓe mai Zaman Kanta ta Ƙasa INEC da ta wallafa takardun shaidar karatu da na cancantar dukkan masu neman muƙaman zaɓe.

Obi ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook, yana mai cewa yin hakan zai ƙara inganta gaskiya da kuma ƙarfafa amincewar jama’a da tsarin zaɓen Najeriya.

Ya ce yayin da yake cike fom ɗin tsayawa takara na INEC, ya lura cewa akwai tambaya da ke neman sanin ko an taɓa ayyana ɗan takara a matsayin wanda ba shi da cikakkiyar lafiyar hankali, lamarin da ya sa ya yi tambaya kan ko shugabannin siyasar ƙasar na nuna halayen shugabanci.

Obi ya ce matsalolin tsaro da tattalin arzikin Najeriya sun fi cancantar a ba su fifiko fiye da siyasa, yana mai cewa sace-sacen mutane, rashin tsaro a manyan hanyoyi da yunwar da miliyoyin ‘yan Najeriya ke fuskanta na buƙatar ɗaukar matakin gaggawa.

Ya ƙara da cewa gwamnati mai nagarta za ta ayyana matsalolin tsaro da na jin-ƙai a matsayin dokar ta-ɓaci tare da haɗa jami’an tsaro, ƙwararru, shugabannin al’umma da sauran masu ruwa da tsaki domin magance su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *