Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya yi gargadin cewa Najeriya na kara fadawa cikin matsalar rashin wadatar abinci.
Ya na mai cewa, kasar ba ta da wani uzuri na shiga matsalar yunwa duk da dimbin albarkatun noma da take da su.
Obi ya fadi hakan ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa ranar Alhamis a shafukansa na sada zumunta, bayan wani gargadi da Majalisar Dinkin Duniya tayi cewa kusan ’yan Najeriya miliyan 35 ke cikin hatsarin fadawa cikin matsananciyar yunwa tsakanin watannin Yuni da Agusta.
Kungiyar jin kai ta Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya ta ce kusan daya daga cikin ’yan Najeriya Bakwai na iya fuskantar matsananciyar karancin abinci, kuma ana sa ran zai fi shafar yankin arewa.
-
Shugaba Tinubu zai gudanar da jawabin Kai tsaye kan ranar dimukuradiyya
-
2027: A barwa Mata Kujerar Mataimakan Gwamna a Jihohi 36
Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa jinkirin kawo dauki zai iya tsananta lamarin, inda iyalai za su rage yawan abincin da suke ci, su sayar da kadarori, ko su fitar da yara daga makaranta don tsanantar ƙaruwar talauci.
“Duk da shekaru Uku na dokar-ta-baci kan abinci da Shugaba Tinubu ya ayyana, haka matsayin Najeriya a jadawalin yunwa ya tabarbare har ta zama cikin kasashe mafi muni a duniya?,” in ji Obi.
Ya kara da cewa, ya ga Najeriya a kan matsayi na 103 a jadawalin na yunwa da majalisar ɗinkin duniyar ta fitar, daga cikin kasashe 123 da aka bincika a shekarar 2022/2023.
Lamarin da ya sauya cikin shekaru 2, zuwa , mataki na 115 daga cikin kasashe 123, a Sh3karun 2025/2026.”
Dan takarar Shugaban kasar ya ce a yanzu an sanya Najeriya cikin kasashen da suka fi fuskantar karancin abinci a duniya, kuma hasashe ya nuna miliyoyin mutane na iya fuskantar matsananciyar yunwa a watanni masu zuwa.