Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta yaba wa Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, bisa bayar da kwafi 140,000 na littattafai bakwai ga ɗakunan karatu na makarantun gwamnati a faɗin Najeriya.

Ma’aikatar ta bayyana wannan gudummawa a matsayin wani muhimmin mataki na inganta al’adar karatu, koyar da kyawawan ɗabi’u da kuma tallafa wa ci gaban yara.

Yayin da yake karɓar littattafan, Ministan Ilimi, Dakta Maruf Tunji Alausa, ya ce wannan shiri ya yi daidai da Shirin Renewed Hope Agenda na Shugaba Bola Ahmed Tinubu

Ya ƙara da cewa gudummawar za ta ƙarfafa ƙoƙarin ma’aikatar na samar da ingantaccen ilimi mai bai wa kowane yaro dama tare da mayar da hankali kan buƙatun ɗalibai a faɗin ƙasar.

Littattafan an samar da su ne ƙarƙashin Shirin Renewed Hope Initiative – RHI tare da haɗin gwiwar gidauniyar Merck Foundation.

Batutuwan da littattafan suka ƙunsa sun haɗa da ilimin yara mata, kare haƙƙin yara, rayuwa mai lafiya, yaƙi da cin zarafin jinsi, lafiyar haihuwa da kuma tarbiyyar zama nagartaccen ɗan ƙasa

Ana sa ran rabon littattafan ga ɗakunan karatu na makarantun gwamnati zai taimaka wajen haɓaka karatu da inganta ilimin ɗalibai, tare da ƙarfafa koyar da kyawawan ɗabi’u da ɗorewar ci gaban yara a Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *