Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ce sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatinsa ta aiwatar sun fara haifar da sakamako mai kyau, inda ya bayyana cewa tattalin arzikin ƙasar na samun daidaito a hankali.

Tinubu ya bayyana hakan ne yayin taron cin abincin dare da ya yi da wakilan kafafen yaɗa labarai na Fadar Shugaban Ƙasa a Abuja.

Ya ce kuɗaɗen shiga na gwamnati sun ƙaru, jihohi na samun ƙarin kaso daga asusun tarayya, ajiyar kuɗaɗen ƙasar a ƙasashen waje ta inganta, yayin da masu zuba jari ke ƙara nuna amincewa da tattalin arzikin Najeriya.

Shugaban ƙasar ya kuma ce an samu ci gaba a fannin tsaro, inda ya bayyana cewa jami’an tsaro sun ƙara ƙaimi wajen yaƙi da ta’addanci, ƴan bindiga, masu garkuwa da mutane da masu satar ɗanyen mai.

Ya ce duk da cewa har yanzu akwai ƙalubalen tsaro, gwamnatinsa ta himmatu wajen tabbatar da zaman lafiya a dukkan sassan ƙasar, tare da gina tattalin arzikin da zai samar wa ‘yan Najeriya ci gaba mai ɗorewa.

 

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *