Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada cewa gwamnatinsa ‘za ta ci gaba da kare ‘yancin aikin jarida da kuma ‘yancin faɗar albarkacin baki kamar yadda Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya tanada.
Da yake jawabi a taron cin abincin dare da ya haɗa shi da wakilan kafafen yaɗa labarai na Fadar Shugaban Ƙasa, Tinubu ya ce dimokuraɗiyya ba za ta bunƙasa ba idan babu kafafen yaɗa labarai masu ‘yanci.
Ya ce gwamnatinsa za ta tabbatar da cewa ‘yan jarida sun samu damar gudanar da aikinsu cikin sauƙi, tare da samun bayanai da kayan aikin da suke buƙata domin sanar da jama’a.
- Gwamnatin Tarayya za ta horas da matasa 5,000 kan gyaran mitocin wutar lantarki
- ‘Yan Sanda sun daƙile yunƙurin barazanar tsaro a harabar Cibiyar NIPSS
Sai dai shugaban ƙasar ya jaddada cewa ‘yancin aikin jarida ba ya nufin yaɗa bayanan ƙarya ko ɓata sunan mutane, yana mai cewa amincewar jama’a na samuwa ne ta hanyar adalci da ƙwarewa da gaskiya da kuma riƙon amana.
Tinubu ya kuma ce gwamnati na ci gaba da mutunta dokar ‘Yancin Samun Bayanai, da sauraren jama’a da sauƙaƙa wa ‘yan ƙasa samun bayanan gwamnati.