Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Plateau ta bayyana cewa a wani samame na  haɗin  gwiwa tsakanin ‘yan sanda da sojoji da sauran jami’an tsaro sun daƙile  wani yunkurin karya tsaro a harabar cibiyar nazarin manufofi da dabarun ƙasa ta Najeriya (NIPSS) da ke Kuru.

A cewar rundunar, lamarin ya faru ne da misalin karfe 11:23 na dare a ranar 1 ga Yuli, 2026, lokacin da jami’an tsaro ke gudanar da sintiri a harabar cibiyar, sun hangi wani mutum ɗauke da makami yana yawo a kusa da ƙofar  shiga ta cibiyar.

Rahotanni sun nuna cewa da mutumin ya ga jami’an tsaron, nan take ya  buɗe  musu wuta sai dai jami’an tsaron sun mayar da martani cikin kwarewa inda suka yi artabu da shi tare da galaba a kansa lamarin da ya kai ga kashe wanda ake zargin.

Haka kuma an ƙwato bindiga ƙirar AK-47 mai lamba 1969003173 daga hannunsa, yayin da aka kai gawarsa dakin ajiye gawa na asibiti domin gudanar da binciken gawa kamar yadda doka ta tanada.

Binciken farko ya nuna cewa mutumin na cikin wata fitacciyar kungiyar masu aikata laifuka, hakan ya sa jami’an tsaro suka ƙara ƙaimi wajen gano tare da cafke sauran mambobin kungiyar, kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Plateau, CP Bassey Ewah ya yaba da jarumta da haɗin kan jami’an tsaro yana mai cewa matakin da suka ɗauka ya hana afkuwar wata babbar barazana ga ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin dabarun ƙasa.
Rundunar ta kuma tabbatar wa mazauna jihar cewa tsarin tsaro a jihar yana nan daram, tare da kira ga jama’a su ci gaba da sanya ido tare da kai rahoton duk wani abu ko mutum da ake zargi ga hukumomin tsaro mafi kusa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *