Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya ce gwamnatinsa ta fara aiwatar da manyan sauye-sauye a fannin kiwon lafiya domin tabbatar da cewa kowane ɗan Najeriya ya samu ingantaccen kula da lafiya ba tare da la’akari da inda yake zaune ko matsayinsa na tattalin arziki ba.
Ya ce gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da shirin sake fasalin harkokin lafiya wanda ya haɗa da farfaɗo da cibiyoyin kula da lafiya na matakin farko da faɗaɗa inshorar lafiya da ƙarfafa rigakafin yara da kuma inganta lafiyar mata da yara.
A cewarsa, an ƙara mutum miliyan shida cikin tsarin inshorar lafiya, ana kuma gyara cibiyoyin kula da lafiya 4,161, inda aka kammala aikin cibiyoyi 3,158
Shugaban ya ƙara da cewa sama da rabin cibiyoyin kula da lafiya na matakin farko a ƙasar suna aiki da yayin da aka yi wa yara sama da miliyan 102 rigakafin kyanda da rubella, sannan ‘yan mata miliyan 17.1 suka samu rigakafin cutar sankarar mahaifa ta HPV.
Haka kuma, an horas da ma’aikatan lafiya 78,054, an ɗauki sabbin ƙwararrun ma’aikatan lafiya 20,000 aiki, tare da kammala ayyukan inganta kayayyakin more rayuwa na kiwon lafiya guda 503 da kuma gina cibiyoyin kula da cutar daji guda uku na zamani.
Tinubu ya ce sauye-sauyen na da nufin ceton rayuka da gina ingantaccen tsarin kiwon lafiya mai ɗorewa, yana mai jaddada cewa inganta lafiyar al’umma na daga cikin manyan manufofin shirin Renewed Hope Agenda kuma gwamnati za ta ci gaba da aiwatar da gyare-gyaren da ta fara.