Shugabannin Gidan Rediyon Blueprint Radio Abuja, sun kai ziyarar aiki ga takwarorin su na Jaridar Blueprint a hedikwatar kamfanin da ke Abuja, domin ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin sassan kafafen yaɗa labaran.

Shugaban Blueprint Radio, Malam Muhammad Kabir Muhammad, ne ya jagoranci tawagar, tare da shugaban sashen labarai da shirye-shirye, Malam Garzali Yakubu, da shugaban sashen gudanarwa da harkokin kuɗi, Misis Adeoye Mobolaji Monisola.

A yayin ziyarar, tawagar ta samu tarba daga Babban Jami’in Gudanarwa na rukunin kamfanin Blueprint, Malam Salisu Umar, tare da Mataimakiyar Shugabar Editoci na Kamfanin, Hajiya Zainab Okino.

Bangarorin biyu sun tattauna kan hanyoyin da za a ƙara inganta haɗin gwiwa da musayar ƙwarewa, domin bunƙasa ayyukan kafafen yaɗa labarai na Blueprint da kuma inganta aikin jarida a Najeriya.

Malam Salisu Umar ya ce Jaridar Blueprint ta fara aiki ne a shekarar 2011, da jaridar mako-mako, kafin daga bisani ta fadada ayyukan ta zuwa jaridar kullum da ake karantawa a ciki da wajen Najeriya.

A hannu guda, ayyukan kamfanin Blueprint ya fadada zuwa bude tashar rediyo ta Blueprint, mai yada shirye-shiryen ta akan mita 105.3 a babban birnin tarayya Abuja.

Tun a ranar 25 ga watan Mayun shekarar 2026 ne kafar rediyon Blueprint ta fara-shirye shiryen gwaji, wanda ake sa ran daga yanzu zuwa kowane lokaci za ta iya dorawa da ayyukan ta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *