Kungiyar Kano Pillars ta tabbatar da naɗin fitaccen kocin Najeriya, Daniel Ogunmodede, a matsayin wanda zai horar da kungiyar a gasar kakar bana ta 2026/27.

An sanar da naɗin a hukumance cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na kungiyar, Isma’eel Abba Tangalashi, ya fitar a shafin sada zumuntar Ƙungiyar a ranar Jumma’a.

Hakan ya kawo ƙarshen cece-kuce kan wanda zai jagoranci kungiyar ta Sai Masu Gida kafin fara sabuwar kakar.

Ogunmodede, wanda ya raba gari daƘungiyar Remo Stars bayan ya jagorancesu lashe gasar NPFL karon farko a tarihin Ƙungiyar a shekaru biyu da suka gabata, ya amince da kwangilar shekara biyu da Kano Pillars, yayin da kakar wasa ta 2026/27 NPFL ke ƙara kusantowa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *