Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya ce sabbin bayanan da suka fito game da Majalisar Presidential Foreign Intervention Promotion Council (PFIPC) sun wuce batun zargin jabun takardu kawai, inda yanzu lamarin ya zama abin da ke jefa sahihancin hukumomin gwamnati cikin shakku.

Atiku ya buƙaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike mai zaman kansa cikin kwanaki bakwai, tare da bayyana sakamakon binciken ga jama’a.

Ya yi gargaɗin cewa idan ba a yi hakan ba, hakan zai ƙara ƙarfafa zargin da jama’a ke yi cewa wasu manyan mutane a cikin gwamnati na iya kasancewa suna da hannu a wannan badakala, kuma akwai yiwuwar an yaudari ‘yan Najeriya da ke neman ayyukan gwamnati ta wata hanya da ake zargin tana samun kariya daga wasu jami’ai.

A cikin wata sanarwa da babban mataimakinsa kan harkokin yaɗa labarai, Phrank Shaibu, ya fitar, Atiku ya ce batun ba wai ko wani mutum guda ya yi jabun takardu ko ya kwaikwayi jami’an gwamnati ba ne kawai, amma yadda wasu hukumomin gwamnati suka amince da ayyukan wata hukuma da Fadar Shugaban Ƙasa ta ce ba ta taɓa wanzuwa ba.

Atiku ya ce bayanin da mai magana da yawun Fadar Shugaban Ƙasa, Bayo Onanuga, ya bayar bai gamsar ba, domin ya haifar da ƙarin tambayoyi maimakon bayar da amsoshi.

Ya ce idan gwamnati na son ‘yan Najeriya su yarda cewa mutum guda ne kawai ya ƙirƙirar wa kansa wata hukuma, ya samu ofis a cikin ginin gwamnati, ya riƙa ganawa da jami’an ƙasashen waje, ya kai ziyara ga EFCC, ya biya albashin ma’aikata ta hanyoyin gwamnati, ya gudanar da asusun hukuma, kuma ya yi duk waɗannan ba tare da sanin ko amincewar wani jami’in gwamnati ba, to wannan bayani ya fi haifar da shakku.

Ya ƙara da cewa idan Adeniyi Adeyemi ya aikata zamba, dole ne ya fuskanci hukunci.

Sai dai babban abin tambaya shi ne yadda tsarin gwamnati ya bari aka gudanar da irin wannan aiki ba tare da an gano shi ba.

Atiku ya ce ko da tarihin wanda ake zargi na iya nuna halayensa, hakan ba zai iya bayyana yadda ya samu damar shiga cikin hanyoyin hukuma ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *