Sufeto Janar na Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya (IGP), Olatunji Rilwan Disu, ya kai ziyarar girmamawa ga Babbar Alƙaliyar Najeriya, Mai Shari’a Kudirat Olatokunbo Kekere-Ekun, a ranar Alhamis, 2 ga Yulin 2026.

An gudanar da ziyarar ne a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya da bangaren shari’a domin inganta gudanar da shari’ar laifuka da tabbatar da bin doka da oda.

A yayin ziyarar, Sufeto Janar ɗin ya yaba da jagorancin bangaren shari’a wajen kare mutuncin kotuna, tabbatar da bin kundin tsarin mulki da kuma gudanar da adalci.

Ya ce rundunar ‘yan sanda da bangaren shari’a abokan aiki ne masu muhimmanci a tsarin shari’ar laifuka, yana mai jaddada cewa akwai buƙatar ci gaba da ƙarfafa haɗin gwiwa domin inganta binciken laifuka, ƙarfafa shirya ƙarar gwamnati a kotu, da kuma tabbatar da cewa ana gudanar da shari’a cikin gaggawa da adalci.

Ya kuma jaddada muhimmancin ingantaccen haɗin kai tsakanin hukumomin biyu wajen ƙarfafa tsarin shari’a da tabbatar da cewa an yi wa kowa adalci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *