Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Najeriya (INEC) ta sanar da tsawaita wa’adin ci gaba da rajistar masu kaɗa ƙuri’a (CVR) na tsawon makonni biyu, bayan nazarin yadda aikin ke gudana da kuma shawarwarin da ta samu daga ofisoshinta na jihohi da jam’iyyun siyasa da ƙungiyoyin fararen hula da sauran masu ruwa da tsaki.

Hukumar ta ce an fara gudanar da rajistar a faɗin ƙasar tun ranar 18 ga Agustan 2025, kuma an shirya kammala ta ne a ranar 10 ga Yulin 2026.

Sai dai yanzu an tsawaita wa’adin zuwa ranar Juma’a 24 ga Yulin 2026, domin bai wa duk waɗanda suka cancanta amma ba su yi rajista ba damar yin hakan.

INEC ta bayyana cewa tsawaita wa’adin na nuna ƙudirinta na tabbatar da cewa kowane ɗan Najeriya da ya cancanci yin rajistar zaɓe ya samu damar shiga kundin masu kaɗa ƙuri’a gabanin zaɓukan da ke tafe.

Haka kuma hukumar ta sanar da ƙaddamar da sabon tsarin rajistar kai-tsaye ta intanet ga waɗanda za su yi rajistar masu jefa ƙuri’a a karon farko.

Hukumar ta ce za a fara amfani da tsarin daga ranar 8 ga Yulin 2026 ta hanyar shafinta na rajista, inda aka tanadi cikakken bayani kan yadda ake amfani da shi.

A cewar INEC, sabon tsarin zai bai wa masu neman rajista damar kammala dukkan matakan yin rajista, har da ɗaukar bayanan tantance mutum (biometric), ta amfani da wayoyinsu ko kwamfutocinsu ba tare da zuwa ofishin hukumar ba. Ta ce an samar da ingantattun hanyoyin tantance bayanai domin kare sahihancin kundin masu kaɗa ƙuri’a.

Hukumar ta buƙaci duk ‘yan Najeriya da suka cancanci yin rajista amma ba su yi ba su yi amfani da ƙarin lokacin da aka bayar tare da sabon tsarin rajistar ta intanet. INEC ta ce za ta ci gaba da inganta tsarin rajistar masu kaɗa ƙuri’a domin tabbatar da sahihanci, adalci da sauƙaƙa wa jama’a shiga harkokin zaɓe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *