Babbar Daraktar Hukumar Kula da Binciken Kuɗi ta Najeriya (NFIU), Hafsat Abubakar Bakari, a ranar 1 ga Yulin 2026, ta kai ziyarar girmamawa ga Shugaban Ƙungiyar Lauyoyin Najeriya (NBA), Afam Osigwe, domin ƙarfafa haɗin gwiwa gabanin tantancewar Najeriya ta shekarar 2027 a tsarin Mutual Evaluation.
Shugabar NFIU ta yaba wa NBA bisa muhimmiyar gudunmawarta wajen taimaka wa Najeriya fita daga jerin ƙasashen dake ƙarƙashin kulawar FATF Grey List, inda ta bayyana fannin shari’a a matsayin muhimmin ɓangare a yaƙi da safarar kuɗaɗe da sauran laifukan kuɗi na haram.
Ta jaddada muhimmancin bayyana gaskiya kan mallakar kamfanoni (beneficial ownership), da rajistar amintattu (trusts) da sauran tsarin shari’a, sannan ta roƙi NBA da ta ware zama na musamman a babban taronta mai zuwa kan batun “Legal Persons and Legal Arrangements.”
- “Hukumar bogi”: Atiku ya buƙaci Tinubu ya binciki badaƙalar
- Sojoji sun kashe mutane shida da ake zargin ’Yan ta’adda ne a Filato
- Oluremi Tinubu ta bai wa ɗakunan karatu na makaranatun Gwamnati littattafai 140, 000
A nasa jawabin, Shugaban ƙungiyar lauyoyi ta ƙasa, NBA, Afam Osigwe ya yaba da ƙoƙarin NFIU wajen ƙarfafa tsarin amincin kuɗaɗen Najeriya, tare da tabbatar da cewa ƙungiyar za ta ci gaba da tallafawa bin ƙa’idojin ƙasashen duniya
Wannan ziyarar ta tabbatar da haɗin gwiwa da aka ƙudura tsakanin NFIU da NBA wajen inganta gaskiya da rikon amana da kuma ƙarfafa tsarin yaƙi da laifukan kuɗi a Najeriya.