Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta buƙaci gwamnatin Côte d’Ivoire ta yi bayani kan musabbabin mutuwar wani ɗan Najeriya, Usama Murtala, bayan da aka tsare shi a gidan yari a ƙasar.

Ministar Harkokin Wajen Najeriya, Ambasada Bianca Odumegwu-Ojukwu, ta kira Jakadan Côte d’Ivoire a Najeriya, Kalilou Traore, zuwa ganawa a ofishinta ranar Juma’a, inda ta kuma buƙaci a biya iyalan marigayin diyya.

Usama Murtala da wasu matasa ‘yan Najeriya biyar—Aliyu Malami da Nasiru Umar da Shamsu Abubakar da Sa’adu Bello da Liman Mohammed—sun yi tafiya daga Jihar Sokoto zuwa birnin Abidjan ta mota domin kasuwanci a watan Agustan bara.

Sai dai bayan sun isa ƙasar, an kama su tare da tsare su a gidan yarin MACA da ke Abidjan ba tare da an gurfanar da su a kotu ko bayyana musu laifin da ake zarginsu da shi ba.

An sake su ne kwanan nan bayan ƙoƙarin da Ofishin Jakadancin Najeriya da Ma’aikatar Harkokin Waje suka yi ta hanyar tattaunawa da shiga tsakani ta diflomasiyya.

Da take karɓar mutanen biyar da suka tsira a Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja , Ministar ta bayyana cewa Gwamnatin Tarayya za ta bi wannan batu da hukumomin Côte d’Ivoire domin neman a biya diyya.

Ambasada Bianca Odumegwu-Ojukwu ta tambayi jakadan Côte d’Ivoire dalilin da ya sa ba a sanar da gwamnatin Najeriya ba lokacin da aka kama tare da tsare mutanen, lamarin da ya jinkirta shiga tsakani ta hanyar diflomasiyya.

Ministar ta buƙaci jakadan ya isar da saƙon ga hukumomin Côte d’Ivoire tare da neman a gudanar da cikakken bincike kan wannan lamari.

Haka kuma ta nemi tabbacin cewa daga yanzu gwamnatin Côte d’Ivoire za ta riƙa mutunta haƙƙoƙi da martabar ‘yan Najeriya da ke shiga ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *