Tarayyar Afirka (AU) ta kira wani taron gaggawa a ranar Juma’a domin tattauna makomar tawagar sojinta da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Somaliya, bayan da Amurka ta sanar da cewa za ta dakatar da muhimmin tallafin da take bayarwa daga shekara mai zuwa.
Washington ta ce ta yanke wannan hukunci ne saboda gwamnatin Somaliya ba ta samu isasshen ci gaba ba wajen daƙile ƙungiyar masu iƙirarin jihadi ta Al-Shabaab, ko kuma karɓar cikakken alhakin tsaron ƙasarta.
A halin yanzu, Somaliya na fuskantar sabon rikicin siyasa bayan da Shugaba Hassan Sheikh Mohamud ya yi wa kundin tsarin mulkin ƙasar kwaskwarima a farkon wannan shekara, wanda ya ba shi damar ƙara wa’adin mulkinsa da shekara guda.
- Gwamnatin Tarayya ta nemi a biya diyya kan mutuwar wani ɗan Najeriya a Côte d’Ivoire
- Sufeto Janar na ‘Yan Sanda ya ziyarci Babbar Alƙaliyar Najeriya, ya nemi ƙarin haɗin gwiwa don inganta tsarin shari’ar laifuka
- Sojoji sun kashe mutane shida da ake zargin ’Yan ta’adda ne a Filato
Jam’iyyun adawa da gwamnatocin wasu yankuna sun yi watsi da sauye-sauyen, lamarin da ya haifar da tashe-tashen hankula a sassa daban-daban na ƙasar, ciki har da babban birnin Mogadishu.
Tawagar Tarayyar Afirka mai kusan sojoji 12,000 na taimaka wa gwamnatin Somaliya da ke da hedikwata a Mogadishu, wajen kare ƙasar da kuma daƙile hare-haren Al-Shabaab, wadda a lokuta da dama ta kusanci mamaye babban birnin.