Kasar Cape Verde na iya zama ƙasa ta biyu mafi ƙanƙanta da ta shiga gasar Cin Kofin Duniya, amma sun bar tasiri mai girman gaske a gasar ta 2026.
Duk da shan kaye a hannun zakaran gasar Cin Kofin Duniya Argentina da ci 3-2 a filin wasa na Miami, ‘yan wasan Blue Sharks sun sace zukatan mutane da dama ganin yadda suka baiwa su Lionell Messi wahala a filin wasa.
Cape Verde ta shiga gasar tana matsayi na 67 a jadawalin FIFA na duniya. Ta yi kunnen doki uku a matakin rukuni – ciki har da rike zakaran Turai Spaniya 0-0 a wasansu na farko, wanda hakan ya zama cikin manyan abubuwan mamaki da gasar Cin Kofin Duniya ta taɓa gani.
-
Kano Pillars ta naɗa Daniel Ogunmodede a matsayin sabon kociyanta
-
NFF ta yaba wa Gwamnatin Tarayya kan ƙaddamar da hukumar yaƙi da miyagun ƙwayoyi a wasanni
Duk da shan kaye, kocin Cape Verde, Bubista, ya bayyana cewa yana cike da alfahari yadda Argentina mai Zakakuran ‘yan wasa a duniya ta tsallake rijiya da baya a hannun tawagarsa.
“Mun nuna cewa ko da mun kasance ƙasa ce ƙarama, za mu iya buga wasa da manyan ƙasashe a duniya,..”Wannan dalili ne na alfahari, in ji shi.
“Mun ajiye tarihi ga ƙasar mu. Ya kamata su yi alfahari da yadda suka wakilci ƙasar mu.
“Yin wasa kamar yadda muka yi da zakaran duniya, da kuma daidaita kwallaye sau biyu, abu ne mai ban mamaki.