Shugaba Bola Ahmed Tinubu a ranar Talata ya ƙaddamar da Kwamitin Aiwatar da Ƙudurin Dokar Aikin ‘Yan Sanda ta Kasa domin shirya tsarin shari’a na aiwatar da tsarin ‘yan sandan jihohi a fadin kasar.
Shugaba Tinubu, wanda Shugaban Ma’aikatansa, Mista Femi Gbajabiamila ya wakilta, ya ƙaddamar da kwamitin ne a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
Ƙaddamarwar ta biyo bayan amincewa da Kudurin Dokar Gyaran Tsarin Mulki (Na ‘Yan Sandan Jiha) na shekarar 2026 da Majalisar Dokoki ta Kasa ta yi, inda Shugaban Ƙasa ya ba da shawarar samar da tsarin tsaro na gida biyu da ya ƙunshi Hukumar ‘Yan Sanda ta Tarayya (Federal Police Service) da kuma Hukumomin ‘Yan Sanda na Jihohi 36 (State Police Services).
Wata sanarwa da Bayo Onanuga, Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman ya sanyawa hannu ta ce Shugaban ya bayyana cewa yayin da gyaran tsarin mulkin yake samar da tsarin ‘yan sandan jihohi, shi kuma Ƙudurin Dokar Aikin ‘Yan Sanda na Kasa zai samar da ingantaccen tsarin shari’a don aiwatar da shi.
- Yara 835,000 aka yi wa allurar rigakafin Cutar Mashaƙo (Diphtheria) a Kano
- Hukumar kula da Jami’an Ƴan Sanda ta Ƙasa (PSC) ta amince da korar manyan jami’an ‘ƴan sanda 4 daga aiki.
- An kori wasu manyan Ƴan Sanda a Najeriy
“Ƙudurin Dokar Gyaran Tsarin Mulki yana kafa harsashin tsarin tsaro na gida biyu, amma ba zai fara aiki kai tsaye ba. Wannan aikin an bar shi ga Ƙudurin Dokar Aikin ‘Yan Sanda na Ƙasa.”
Ya ce dokar da aka duba za ta magance batutuwan da suka zama dole domin gudanar da tsarin ‘Yan Sandan Jiha cikin sauki.
“Ƙudurin Dokar Aikin ‘Yan Sanda na Ƙasa da aka shifta zai kunshi tanadi kan mafi kankantar ka’idojin aikin ‘yan sanda, tantance shirye-shiryen jihohi, haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya da jihohi, gaskiya da rikon amana, kiyaye hakkin dan adam, da kuma yanayin tattalin arziki.”
Shugaban ya ce kwamitin zai samar da daftarin doka da ke a shirye don aiwatarwa nan da nan bayan kammala tsarin gyaran tsarin mulkin.
“An kafa Kwamitin Aikin ne domin samar da daftarin Kudurin Dokar Aikin ‘Yan Sanda na Ƙasa da ke da inganci ta fannin fasaha kuma a shirye yake don aiwatarwa kafin a miƙa shi ga Majalisar Dokoki ta Ƙasa,” in ji Tinubu.
Ya ce kwamitin yana da muhimmanci domin kauce wa jinkiri bayan an amince da Ƙudurin Dokar ‘Yan Sandan Jiha.
“Kada mu jira har sai an kammala tsarin gyaran tsarin mulki kafin mu fara wannan muhimmin aiki,” in ji shi.
Membobin Kwamitin sun haɗa da Mista Femi Gbajabiamila, wanda zai kasance shugaban kwamitin.
Sauran membobin sun hada da Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma Ministan Shari’a da Shugaban Kungiyar Lauyoyin Najeriya (NBA) da Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) da Mai Ba da Shawara kan Tsaron Kasa (NSA) da kuma Shugaban ‘Yan Sandan Ƙasa (IGP) sa shugaban KungiyarGwamnonin jihohi.