Shugaban Hafsan Sojojin Najeriya, Laftanar Janar Waidi Shu’aibu, ya ce rundunar sojin Najeriya za ta cigaba da fadada ayyukan ta a yankin Kudu maso Gabashin ƙasar.
Yayin wata ziyarar aiki da ya kai sansanin sojin Nkwagu da ke Abakalikin jihar Ebonyi a ranar Alhamis, Waidi Shaibu, yace manufar rundunar ta ginu ne akan ƙwarewa da jajircewa, ta fuskar tunkarar ƙalubalen tsaro a zamanance.
Yayin ganawar Hafsan da manyan jami’ai da sauran dakaru, Laftanar Janar Shaibu ya shaida musu cewar ziyarar ta sa, na da alaƙa da ƙarfafa musu gwiwar ayyukan sadaukarwar da suke yi a kullum, domin tabbatar da zaman lafiyar ƙasar.
- Sojoji sun daƙile harin ISWAP kan sansanin Logomani
- Operation Haɗin Kai ta ceto ƙarin waɗanda aka sace, ta daƙile harin ISWAP a Borno
Ya kuma buƙace su da su ci gaba da kasancewa cikin shiri, tare da cigaba da mutunta tsarin Mulki da dokokin da suka kafa aikin, da kuma mutunta haƙƙin dan-adam yayin da suke ci gaba da matsa lamba kan masu barazana ga zaman lafiya da tsaron yankin.
Ziyarar da Hafsan ya kai ta kasance wani ɓangare na ƙoƙarin ganewa idon sa shirin da rundunar ta yi, ta fuskar dabarun yaƙi, da ƙwarewar aiki da kuma walwala.
