Rundunar haɗin gwiwa ta Operation Hadin Kai (OPHK) ta sanar da samun sabbin nasarori a yaƙin da take yi da ƙungiyoyin ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas, inda ta ceto ƙarin mutane da aka sace tare da dakile wani hari da mayaƙan ISWAP suka kai sansanin soji da ke Logomani a jihar Borno.
A cikin wata sanarwa da Muƙaddashin Jami’in Yaɗa Labarai na rundunar, Kyaftin Mohammed Goni, ya fitar, ya ce a ranar 7 ga Yuli, 2026, sojojin Bataliya ta 115 sun ceto ƙarin mutane biyu daga maboyar ‘yan ta’adda a ƙaramar hukumar Askira/Uba.
- NIMC ta fara rajistar NIN a mazaɓu 8,809 na ƙasar
- NOA ta yi alƙawarin wayar da kan jama’a kan rajistar NIN
Sanarwar ta ce yayin aikin, sojojin sun kuma ƙwace kuɗi har Naira miliyan 1.2 da ake zargin haramtun kuɗaɗen ne, tare da kayan abinci da sauran kayayyakin da ake amfani da su wajen tallafa wa ayyukan ta’addanci.
Ta ƙara da cewa an kai waɗanda aka ceto wurin da ya dace domin ba su kulawar lafiya da kuma tallafin ƙwararrun likita.