Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), a ranar Laraba, ya yi gargaɗi ga jami’an tsaro da aka tura don yaƙi da ta’addanci da fashi da makami da kada su yi jinkirin tunkarar ƴan ta’adda, yana mai cewa duk jami’in da ya jira umarni kafin ya ɗauki mataki za a ɗauke shi a matsayin ɗan ta’adda.

Yayin da yake jawabi a wajen ƙaddamar da motoci masu sulke guda 62 da babura sama da 300 da gwamnatin jihar Sokoto ta saya wa hukumomin tsaro, Musa ya ce dole ne dakarun su ɗauki kwararan matakai kan miyagun abubuwa a cikin ƙa’idojin aiki.

“Duk wanda ya ƙi harbin ɗan ta’adda da sunan jiran umarni, za mu ɗauke shi kamar ɗan fashi da makami,” in ji shi.

Ministan ya kuma gargaɗi jami’an tsaron game da tsangwama ko karɓar kuɗi na guri (na goro) a hannun jama’a, inda ya jaddada cewa an tura su ne don kare ƴan ƙasa masu bin doka ba don tsoratar da su ba. Ya buƙace su da su nuna kwarewa, horo, da riƙon amana yayin gudanar da ayyukansu.

Musa ya bayyana sayen kayayyakin tsaron a matsayin babban tallafi ga tsarin tsaron jihar, yana mai cewa motocin da baburan za su haɓaka zirga-zirga da ingancin ayyukan hukumomin tsaro wajen mayar da martani ga fashi da makami, ta’addanci, garkuwa da mutane, da sauran manyan laifuka na tashin hankali.

Ya bayyana cewa ƙalubalen tsaron ƙasar na ci gaba da sauyawa, inda ƴan ta’adda da sauran miyagu ke sauya dabaru tare da amfani da mawuyacin yanayi na ƙasa (daji).

Musa ya ƙara da cewa dole ne martanin hukumomin tsaro shi ma ya sauya ta hanyar inganta zirga-zirga, ayyuka dabarun sirri, da ingantaccen haɗin gwiwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *