Babban Daraktan Hukumar Asusun Bunƙasa Kayayyakin Iskar Gas ta Tsakiya da Ƙasa (MDGIF), Oluwole Adama, ya jaddada muhimmancin bunƙasa kasuwar iskar gas ta cikin gida domin haɓaka tattalin arziki da ci gaban masana’antu a Najeriya.
Adama ya bayyana haka ne yayin wani zaman tattaunawa mai taken “Bunƙasa Kasuwar Iskar Gas ta Cikin Gida domin Haɓaka Tattalin Arziki da Ci Gaba”, a rana ta uku ta taron Makon Makamashin Mai da Gas na Najeriya (NOG Energy Week 2026), da aka gudanar a Cibiyar Taro ta Ƙasa da Ƙasa (ICC) da ke Abuja.
Ya ce ƙara zuba jari a kayayyakin more rayuwa na iskar gas, da inganta damar shiga kasuwa da kuma haɗin gwiwa tsakanin gwamnati, da masu zuba jari da kamfanoni masu zaman kansu zai taimaka wajen cin gajiyar ɗimbin albarkatun iskar gas da Najeriya ke da su.
- NOA ta yi alƙawarin wayar da kan jama’a kan rajistar NIN
- Gwamnonin Arewa sun ƙaddamar da asusu kan tsaro
- NIMC ta fara rajistar NIN a mazaɓu 8,809 na ƙasar
Adama ya ƙara da cewa bunƙasa kasuwar iskar gas zai ƙarfafa samar da makamashi, da haɓaka masana’antu da samar da ayyukan yi da kuma inganta gasa a tattalin arziƙin ƙasar.
Ya kuma tabbatar da cewa hukamar MDGIF za ta ci gaba da tallafa wa zuba jari a fannin iskar gas ta hanyar sabbin hanyoyin samar da kuɗi da haɗin gwiwa, domin cimma manufofin Gwamnatin Tarayya na Shekarun Iskar Gas (Decade of Gas Initiative) da kuma sauyin amfani da makamashi.