Kyaftin ɗin Newcastle Bruno Guimaraes ya sanar da ƙungiyar cewa yana son komawa Arsenal da taka leda.
Sai dai Newcastle ba su ce komai ba kan lamarin, amma kafar Sky Sports News ta fahimci cewa Arsenal ba su taɓa tuntuɓar Newcastle ba game da samun ɗan wasan tsakiyar.
Guimaraes yana da sauran shekaru 2 a kwantiraginsa da Newcastle, tare da zaɓin tsawaitawa da shekara guda har zuwa bazara ta 2029.
-
Gasar Cin Kofin Duniya: Kocin Masar Ya Zargi FIFA Da Alƙali Da Nuna Wa Argentina Bambanci
-
Argentina ta samu nasarar kan Masar da ci 3-2
-
Ronaldo, Neymar da sauran taurari sun yi bankwana da gasar Kofin Duniya har abada
Newcastle ba su da sha’awar sayar da ɗan wasan ɗan asalin Ƙasar Brazil, inda suka dage cewa kyaftin ɗin su ba na sayarwa ba ne kuma ba sa maraba da wani tayi.
Guimaraes, wanda ya koma Newcastle daga Lyon kan fam miliyan 35 a watan Janairun 2022, ya zama ɗaya daga cikin manyan ‘yan wasan da suka taimaka wajen dawo da martabar ƙungiyar bayan masu zuba hannun jari daga Saudiyya suka kammala sayen ƙungiyar a watan Oktobar 2021.