Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana ƙaddamar da kwamitin gudanar da asusun tsaro na Arewa a matsayin babban mataki na farko wajen cika alƙawarin gwamnonin na tunkarar tabarbarewar tsaro da ke ƙara ta’azzara a faɗin Arewa.
Gwamnan ya bayyana cewa asusun amintaccen tsao na Arewa zai samar da kyakkyawan tsari na tara kuɗaɗe, ƙarfafa musayar bayanan sirri, da tallafawa hukumomin tsaro a yaƙin da ake yi da rashin tsaro.
“Ƙaddamar da Kwamitin Amintattu na yau ya zama babban mataki na farko wajen tabbatar da ƙudurin wannan ƙungiyar na tunkarar mummunan rashin tsaro da ke addabar yankinmu a cikin tsari na bai-ɗaya, haɗin kai, dorewa, da kuma riƙon amana,” in ji Yahaya.
- Gasar Cin Kofin Duniya: Kocin Masar Ya Zargi FIFA Da Alƙali Da Nuna Wa Argentina Bambanci
- Shugaba TIinubu ya ƙaddamar da Kwamitin Aiwatar da Ƙudurin Dokar aikin ‘yansanda ta ƙasa
- Yara 835,000 aka yi wa allurar rigakafin Cutar Mashaƙo (Diphtheria) a Kano
Gwamna Yahaya ya bayyana cewa tun farko jihohi 19 sun amince a Kaduna da Abuja don kafa asusun bayan sun fahimci cewa ƙalubalen tsaron da ke fuskantar yankin yana buƙatar mataki na gaggawa da na haɗin gwiwa.
Yayin da yake amincewa da nauyin da tsarin mulki ya ɗora wa gwamnatin tarayya na samar da tsaron ƙasa, Yahaya ya ce dole ne jihohin Arewa su tallafa wa ƙoƙarin tarayya ta hanyar inganta tattara bayanan sirri da juriya ta al’umma, da haɗin gwiwar shiyyoyi.
Ya yi gargaɗin cewa kada asusun ya zama wani tsari na tsatson mulki ko jan ƙafa (bureaucracy), a’a, ya kamata ya kawo ingantaccen sauƙi da za a iya auna shi a fannin tsaro, martani cikin gaggawa, da kiyaye rayuka da dukiyoyi.
Za a iya tunawa cewa gwamnonin Arewa a baya sun naɗa tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Yayale Ahmed, da tsohon Babban Hafsan Tsaron Ƙasa, Janar Martin Luther Agwai (mai ritaya) a matsayin shugabannin haɗin gwiwa na Kwamitin Amintattu na Asusun Amintaccen Tsaro na Arewacin Najeriya (NNSTF).
An ƙaddamar da kwamitin ne a ranar Laraba a Kaduna yayin taron, inda aka naɗa tsohon Babban Sauron Ƴan Sanda da Usman Alkali Baba da tsohon Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Lt.-Gen. Faruk Yahaya (mai ritaya), da sauran fitattun masu ruwa da tsaki na Arewa a matsayin mambobi.
An tsara NNSTF ne don tara albarkatu, haɓaka tsarin haɗin gwiwar tsaro, da ƙarfafa musayar bayanan sirri domin tallafawa hukumomin tsaro na tarayya.