Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa, mutane shida da ake zargin mayaƙan ISWAP ne tare da iyalansu sun miƙa wuya ga sojojin Bataliya ta 192 a Borno.
Cikin wata sanarwa da Rundunar Operation haɗin Kai ta fitar a ranar Laraba 9 ga watan Yulin shekarar 2026, Rundunar ta ce ta gano wasu ƙarin bayanai game da ƙungiyar ta ISWAP.
Binciken farko da ɓangaren leƙen asiri na rundunar sojin ya gano na nuni da cewa mayaƙan sun tsere ne daga wasu sansanonin ‘yan ta’adda da ke yankunan Guduf da Chikide, a tsaunukan Mandara na ƙaramar hukumar Gwoza.
Rundunar ta ce an samu kuɗi sama da Naira miliyan 1.54 da wayoyin salula guda biyu a hannunsu.
- Operation Haɗin Kai ta ceto ƙarin waɗanda aka sace, ta daƙile harin ISWAP a Borno
- Sojoji sun kama masu kai wa ‘yan ta’adda kayan tallafi
- Sojoji sun daƙile harin ISWAP kan sansanin Logomani
Rundunar ta kuma bayyana cewa ta kama wani da ake zargin mai kai wa ‘yan ta’adda magunguna ne a shingen bincike na Molai.
Sannan a yankin Tarmuwa na jihar Yobe an sake kama wani da tayoyin babura guda biyar da ake zargin zai kai wa ‘yan ta’adda ne.
Rundunar ta yi gargaɗin cewa waɗanda ke baiwa yan ta’addar tallafi ko wata gudummawa su kuka da kansu, domin gujewa fuskantar hukunci mai tsanani.
A baya bayan nan dai rrundunar na ci gaba da faɗaɗa hare-haren da take kaiwa a yankunan dake kan iyaka da tafkin chadi, tare da matse hanyoyin zirga-zirga ga masu tayar da ƙayar baya.