Rundunar Operation Haɗin Kai ta sanar da cafke wani fitaccen mai aikata laifi a ƙaramar hukumar Gombi ta jihar Adamawa bayan samun bayanan sirri.
Ta ce binciken da aka gudanar bayan kama mutumin ya kai ga gano bindiga kirar AK-47 guda ɗaya da harsasai 28.
- Kada ku jira umarni kafin ku harbi ‘yan ta’adda, Janar Christopher
- Operation Haɗin Kai ta ceto ƙarin waɗanda aka sace, ta daƙile harin ISWAP a Borno
Haka kuma, sojojin Bataliya ta 149 sun kama mutane biyu da ake zargin masu kai wa ‘yan ta’adda kayan tallafi ne a ƙaramar hukumar Mobbar ta jihar Borno.
Rundunar ta an ƙwace kuɗaɗe da mota ƙirar Volkswagen Golf da kayan gini da kayan gida da sauran kayayyakin da ake zargin an tanade su ne domin kaiwa ‘yan ta’adda.