Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sanar a ranar Litinin, 13 ga Yulin 2026, cewa Amurka ta sake ƙaƙaba katangar ruwa (naval blockade) kan Iran, yana mai cewa Mashigin Hormuz zai ci gaba da kasancewa a buɗe “ko da Iran ta amince ko ba ta amince ba.”

Trump ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Truth Social.

“Mashigin Hormuz a buɗe yake, kuma zai ci gaba da kasancewa a buɗe, da ko ba tare da Iran ba. Muna sake kafa katangar ruwa kan Iran, wacce za ta hana jiragen ruwan Iran da kwastomominta shiga ko fita.

Amma duk sauran ƙasashe za su ci gaba da amfani da mashigin cikin ‘yanci da adalci.” Inji shi.

Trump ya kuma sanar da cewa daga yanzu Amurka za ta riƙa kiran kanta “Mai Kare Mashigin Hormuz”.

Ya ce saboda aikin tabbatar da tsaro a wannan muhimmin mashigin ruwa, Amurka za ta karɓi kashi 20 cikin ɗari na kuɗin jigilar duk wani kaya da za a shigar.

Har zuwa lokacin wallafa wannan rahoto, ba a samu wata sanarwa daga gwamnatin Iran ko wasu ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa kan wannan sabon matakin da Trump ya sanar ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *