Sabon Sakatare Janar na Ƙungiyar Ƙasashen Larabawa Nabil Fahmy a ranar Litinin ya yi kira ga Iran da ta daina kai hare-hare kan ƙasashen Larabawa tare da mutunta ikon mallakarsu, yayin da kuma ya soki Isra’ila kan hana wata tawaga shiga Gabar Yamma da aka mamaye.
Nabil ya bayyana hakan ne a jawabinsa na farko a matsayin sabon shugaban ƙungiyar ta ƙasashen Larabawa a birnin Alƙahira
“Mutunta ikon mallakar ƙasashen Larabawa wata muhimmiyar ƙa’ida ce da ba za mu amince da take ta ba,” in ji shi, yana mai cewa hare-haren da Iran ke kai wa ƙasashen Gabas ta Tsakiya na daga cikin manyan barazanar da yankin ke fuskanta.
- ‘Yan Houthi sun harba makamai masu linzami zuwa Saudiyya
- Abubuwan ban-mamaki 5 game da Sheikh Hamad bin Khalifa Al Thani
- Hurmuz zai ci gaba da kasancewa a bude duk da barazanar Iran – Trump
“Na sake maimaitawa karo na uku: Duk wata barazana ga tsaron kowace ƙasa ta Larabawa, barazana ce ga tsaron dukkan ƙasashen Larabawa.”
Fahmy ya ce duk da Isra’ila ba ta ba shi izinin shiga Gabar Yamma da aka mamaye domin ganawa da Shugaban Falasɗinu Mahmoud Abbas ba, za su ci gaba da ƙoƙarin yin hakan.
A cewar Fahmy “Batun Falasɗinu zai ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin manyan abubuwan da ƙungiyar za ta ba fifiko, kuma ɗaya daga cikin abubuwan da ni kaina zan fi mayar da hankali a kai.”
Jami’in diflomasiyyar na Masar ya fara wa’adin jagorancinsa ne a daidai lokacin da rikice-rikice ke ƙara ƙamari a yankin.
Yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin Amurka da Iran na fuskantar barazana, yayin da hare-haren Amurka kan Iran da kuma hare-haren Iran kan ƙasashen Larabawan Tekun Fasha suka sake dawowa.
A lokaci guda kuma, yaƙe-yaƙe na ci gaba a wasu ƙasashen Larabawa kamar Lebanon, Zirin Gaza da Sudan.