Kasar Spaniya za ta buga wasan karshe na Gasar Cin Kofin Duniya a karo na farko tun bayan shekara ta 2010, bayan ta doke Faransa da ci 2-0.
Dan wasa Mikel Oyarzabal ya ci gaba da nuna bajinta yayin da Pedro Porro ya ci kwallo ta biyu da ta tabbatar musu da nasara a kan Faransawa a filin wasa na Dallas.
Yanzu Spaniya za ta jira wanda zai yi nasara tsakanin Ingila da Argentina domin fafatawa a wasan karshe na ranar Lahadi, yayinda Faransa za ta buga wasan neman matsayi na 3 a ranar Asabar, wannan ya kawo ƙarshen zaman shekaru 14 na Koci Didier Deschamps.
- AFCON 2027: Guinea ta buƙaci a sauya wurin wasanta da Afirka ta Kudu
- Super Falcons za su gwada karfi da Black Queens na Ghana a wasan sada zumunta
- Gasar Cin Kofin Duniya: Kocin Faransa ya magantu kan raunin Kyalian Mbappe
Spaniya ta ci kwallo na farko da bugun fenareti bayan Lucas Digne, ya bugi Lamine Yamal, ba da niyya ba a ƙoƙarin sa na fidda ƙwallon waje.
Bayan haka, Oyarzabal ya zura kwallo ta biyu a minti na 22, wannan shi ne kwallonsa ta 5 a gasar.
Da haka ne Spaniya mai rike da Kofin Turai, ta tsallake zuwa wasan karshe na Kofin Duniya ta 2026.