Gwamnatin Tarayya ta ɗaukaka watan Disamba na shekarar 2028 a matsayin rukunin ƙarshe na sauyawa daga tsarin watsa shirye-shiryen talabijin na analogu zuwa tsarin dijital.
Babban Daraktan Hukumar Kula da Kafafen Yaɗa Labarai ta Ƙasa (NBC), Charles Ebuebu, shi ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa (NAN) a birnin Abuja ranar Talata.
Ebuebu ya bayyana cewa wa’adin watan Disamba na 2028 shi ne zai zama silar daina amfani da tsarin analogu gaba ɗaya. “Mun sanya ajali na daina amfani da tsarin analogu. Kafin lokacin, za a samar da abubuwa da dama. Wannan shi ne rukunin farko kawai,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa rukunoni na gaba za su haɗa da tsarin talabijin na kuɗi (pay TV), bunƙasa gidajen studio, da kuma samar da wuraren da aka keɓance don masu shirya fina-finai da shirye-shirye.
- Masu garkuwa da mutane sun sace shugaban makaranta, Jami’in NECO, da ɗalibai a Kogi
- Celtic ta yi wa Iheanacho tayin sabon kwantaragin shekara biyu bayan lashe kofin gasar
- Manchester United na neman dan wasan gaban Arsena
Shugaban na NBC ya bayyana cewa ana samun ci gaba wajen auna yawan masu kallo, inda aka kammala gwajin tsarin a gidaje kusan 7,000 a birnin Ikko (Lagos), yayin da aka fara aiwatar da tsarin a Abuja.
A cewarsa, hukumar za ta bayyana matakan ga jama’a bayan ta tattauna da manyan masu ruwa da tsaki, ciki har da Ƙungiyar Kafafen Yaɗa Labarai ta Najeriya (BON), don samun goyon bayansu.
Ya bayyana cewa daina amfani da tsarin na analogu zai ‘yantar da hanyoyin watsa shirye-shirye (spectrum) masu kima don amfanin sauran fannoni, yana mai bayyana hakan a matsayin wata muhimmiyar dukiya ga ƙasa.
Ebuebu ya ƙara da cewa masana za su kimanta ƙimar wannan spectrum ɗin kafin a raba shi ga masu amfani da shi kamar kamfanonin sadarwa, na manhajoji, da na harkokin kuɗi.
Ya ce: “Ba zan bayyana takamaiman adadin kuɗin ba, amma an ƙiyasta ƙimarsa ta haura dala biliyan 50. Masana ne za su ƙayyade ainihin ƙimarsa kafin a raba shi,” in ji shi.
Dangane da tsofaffin kayan aiki na watsa shirye-shirye kuwa, Ebuebu ya bayyana cewa hukumar tana tsara wata manufa da ta ginu bisa shawarwarin masana da kuma kyawawan tsare-tsare na duniya.
Ya bayyana cewa takardar tsarin sauya sheka zuwa dijital (Digital Switch Over White Paper) ta buƙaci kafofin yaɗa labarai da su raba aikin shirya bidiyo daban, sannan aikin tura shi zuwa ga masu kallo ya zama na musamman, inda kamfanonin rarraba saƙo kamar NIGCOMSAT za su riƙa gudanar da hakan.
A cewarsa, ana iya sauya wa tsofaffin kayan aikin analogu mazauni don amfani da su a wani fannin daban idan ta yiwu, yayin da za a tuntuɓi gwamnati don ta karɓe kayayyakin da ba za su ƙara amfanar ba, domin kare aukuwar haɗarin gurbatar muhalli da ke tasowa daga sharar masana’antu.