Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a ranar Talata ya ƙaddamar da rukunin samar da ruwan sha na Bwari (Bwari Township Water Supply Network) a Babban Birnin Tarayya (FCT), inda ya sake jaddada ƙudirin gwamnatinsa na samar da ruwan sha ga al’ummomin da ba su da shi a faɗin babban birnin ƙasar.
Shugaban ƙasar, wanda Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu ta wakilta a wajen taron da aka gudanar a Dandalin Kasuwar Bwari (Bwari Market Roundabout), ya bayyana aikin a matsayin gagarumin ci gaba a ƙarƙashin Tsarin Sabon Fata (Renewed Hope Agenda), inda ya yi alƙawarin cewa za a miƙa irin wannan aikin samar da ruwa kafin ƙarshen wa’adin mulkin gwamnatinsa.
Tinubu ya bayyana cewa samar da tsaftataccen ruwa na ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da gwamnatinsa ta sanya a gaba don tabbatar da ci gaba mai ma’ana, yana mai cewa mazauna yankunan karkara sun cancanci samun irin abubuwan more rayuwa da ake da su a tsakiyar birni.
“Tsarin Sabon Fata ba kawai taken baki ba ne. Yarjejeniya ce. Sadaukarwa ce ta gaske, tsari ne da aka lissafo kuma ba za mu yi ƙasa a gwiwa ba wajen samar da shugabanci na gari ga al’umma,” in ji shi.
- Kotu: Malami ya kasa tabbatar da asalin kuɗin sayen kadarori 48
- Bayan watanni shida, EFCC ta samu nasarar ƙwace kadarorin da ake alaƙanta da ga Malami
- Gasar Cin Kofin Duniya: Messi ya jagoranci Argentina zuwa wasan karshe bayan doke Ingila 2-1
A cewar Shugaban ƙasar, gwamnatinsa ta ƙuduri aniyar kawo ƙarshen rashin daidaiton ci gaba da aka shafe shekaru da dama ana yi a FCT ta hanyar tabbatar da cewa ba a mance da yankunan karkara da na kewaye ba wajen samar da muhimman abubuwan more rayuwa.
“An daɗe ana kallon Abuja a matsayin birni mai fuska biyu—tsakiya mai sheƙi da kuma yankunan karkara da aka bari a baya. Mun ce a’a. Wannan zamanin ya wuce. Najeriya ta kowa ce, kuma dole ne a rarraba ci gaba zuwa kowane sassa,” in ji shi.
Tinubu ya tuna cewa bayan ya duba shawarar da Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike ya gabatar, ya bayyar da umarnin a gudanar da aikin ba tare da ɓata lokaci ba domin magance matsalolin ruwa da mazauna Bwari, Ushafa da sauran yankunan maƙwabta ke fuskanta.
Ya ce sabon rukunin samar da ruwan da aka kammala, wanda kamfanin China Geo-Engineering Construction (CGC) Limited ya gudanar, zai haɗa garin Bwari da sauran al’ummomin da ke maƙwabtaka da su kai tsaye da tsaftataccen ruwan sha daga Dam ɗin Lower Usuma Dam.