Shugaban Majalisar Wakilai, Dakta Abbas Tajudeen,GCON, ya gabatar da wasu shawarwari kan yadda za a aiwatar da tsarin kafa rundunar ‘yan sandan Jihohi domin inganta tsaro a Najeriya.
Ya yabawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa gabatar da kudirin gyaran kundin tsarin mulki da zai ba da damar kafa rundunonin ‘yan sandan Jihohi, yana mai cewa wannan wani muhimmin mataki ne na gyaran tsarin tsaro a ƙasar.
Da yake jawabi a taron tattauna batutuwan tsaro na Majalisar Dokoki ta Ƙasa a ranar Laraba, Abbas ya ce ya kamata a fara kafa ƙa’idojin aiki kafin a fara samar da rundunonin ‘yan sandan jihohi.
-
Majalisar Wakilai ta soke tsohon kudirin ‘Yan Sandan Jihohi, ta fara duba kudirin Tinubu
-
‘Yan sanda a Kano sun kama wanda ake zargi da kai wa ‘yan bindiga makamai a Bichi
Ya kuma ba da shawarar a aiwatar da tsarin a hankali daga jiha zuwa jiha, tare da tabbatar da cewa an samar da ingantaccen tsarin kuɗaɗen gudanarwa domin kauce wa matsalolin rashin albashi da ka iya shafar aikin jami’an tsaro.
Shugaban Majalisar ya ce, duk da cewa Majalisar Dokoki ta Ƙasa tana ci gaba da ware kuɗaɗe ga hukumomin tsaro, kuɗi kaɗai ba su isa su magance matsalolin tsaro ba. Ya jaddada bukatar samar da tsarin bayanan masu aikata laifuka da na bayanan halittu na ƙasa baki ɗaya, da kuma inganta musayar bayanan sirri da haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro.
Abbas ya bayyana cewa ƙasar da ke da yawan jama’a sama da miliyan 200 ba za ta iya dogaro da rundunar ‘yan sanda ta tarayya kaɗai ba wajen kula da tsaro.
Ya ce matsalolin tsaro na yankuna suna buƙatar jami’an da suka san al’ummomin da suke aiki a cikinsu, domin hakan zai ƙara amin cewa tsakanin jama’a da masu tsaron su.

Sai dai ya amince cewa akwai fargabar da wasu ke da ita na yiwuwar Gwamnoni ko masu ruwa da tsaki su yi amfani da rundunar ‘yan sandan jihohi ta hanyar da ba ta dace ba. Ya ce kudirin dokar ya tanadi matakan kariya, ciki har da nada Kwamishinan ‘Yan Sanda na jiha bisa shawarar Majalisar ‘Yan Sanda ta Ƙasa, tare da amincewar Majalisar Dokokin jihar, yayin da cire shi zai buƙaci rinjayen kashi biyu bisa uku na ‘yan majalisar.
Abbas ya kuma bukaci Najeriya ta yi nazari kan yadda ƙasashe irin su Jamus, Kanada da Amurka suka tsara tsarin ‘yan sandansu, yana mai cewa darasin da ake koya daga waɗannan ƙasashe shi ne cewa nasarar ‘yan sandan jihohi tana dogara ne kan ƙa’idoji na ƙasa, musayar bayanai da kuma cikakken tsarin tabbatar da ɗaukar alhaki. Ya ce idan aka aiwatar da waɗannan matakai, za a samu tsarin tsaro mai inganci da zai amfanar da ‘yan Najeriya.