Tawagar ‘yan wasan Najeriya ‘yan kasa da shekaru 20 Flying Eagles, za ta kara da Black Satellites na Ghana, da Junior Sparrow Hawks na Togo, da kuma Young Stallions na Burkina Faso a matakin rukuni na gasar (WAFU B U20) ta bana da za a gudanar a Cote d’Ivoire.

Jadawalin da aka yi ranar Laraba ya sanya Flying Eagles da abokan hamayyar su a Rukuni na B.

Mai masaukin baki, Cote d’Ivoire, ta na cikin rukuni na ‘A’ tare da Jamhuriyyar Benin da kuma Jamhuriyyar Nijar.

Kocin ‘yan Najeriya, Abdu Maikaba da ‘yan wasan sa 23 za su bar ƙasar a ranar Litinin mai zuwa, don farantawa ‘yan Najeriya rai ta hanyar ɗaukar ɗaya daga cikin tikiti 2 na WAFU B zuwa gasar ‘yan kasa da shekaru 20 na nahiyar Afirka ta bana mai zuwa da za a buga a Ghana.

Flying Eagles dai sun lashe wannan gasa ta Afirka sau 7, kuma sun lashe kyautar azurfa ta Kofin Duniya sau 2, sa’an nan kuma sune masu rike da kofin WAFU B U20 a yanzu.

A karo na ƙarshe da aka buga gasar a Lome a 2024, sun doke Satellites na Ghana da ci 2-1 a wasan karshe.

Yanzu kuma za su fara da kare kambun su a Cote d’Ivoire.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *