Idan ba a manta ba, a ranar Juma’a wani hatsarin motar bas ya yi sanadin mutuwar yara 20 da babban mutum guda a gundumar Kapchorwa da ke ƙasar Uganda, yayin da suke dawowa daga yawon shakatawa.

A yanzu, gwamnatin Uganda ta sanar da dakatar da duk wani yawon buɗe ido da tafiye-tafiyen makarantu a faɗin ƙasar har sai an kammala bincike kan musabbabin hatsarin.

Ministan Ilimi na Uganda, John Chrysostom Muyingo, ya ce an ɗauki matakin ne domin kare lafiyar ɗalibai, yayin da hukumomi ke ci gaba da binciken yadda hatsarin ya faru.

Binciken farko na ‘yan sanda ya nuna cewa direban motar ya rasa ikon sarrafa ta, yayin saukowa daga wani tudu, inda motar ta kauce daga hanya, ta bugi wani babban dutse sannan ta kife.

Lamarin ya sake jawo hankalin jama’a kan matsalar haɗurran ababen hawa a Uganda, inda gwamnati ta ce za ta sake nazarin matakan tsaron zirga-zirgar motocin makarantu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *