Yayin gabatar da Abdul Maikaba, sabon kocin Bayelsa United.

Kungiyar Bayelsa United ta ƙaddamar da kocin tawagar Flying Eagles ta Najeriya, Abdul Maikaba, a matsayin sabon mai horas da ƙungiyar gabanin kakar wasa ta 2026/2027 na gasar NNL.

Maikaba zai jagoranci ƙungiyar da ke Yenagoa yayin da shirye-shiryen fara sabuwar kakar wasa ke ci gaba, inda mahukuntar ƙungiyar ke fatan ƙwarewarsa za ta taimaka wa ƙungiyar wajen cimma burinta.

Maikaba wanda a halin yanzu shi ne kocin tawagar ‘yan ƙasa da shekaru 20 na Najeriya, ya taba horas da manyan ƙungiyoyi a gasar NPFL da dama inda ya samu nasarori.

Daga cikin ƙungiyoyin da ya taba horaswa akwai Wikki Tourists da Plateau United da Akwa United da Enyimba FC da Enugu Rangers da kuma Kano Pillars.

Wannan ƙaddamarwa na nufin buɗe sabon babi ga Maikaba da Bayelsa United yayin da suke shirin fuskantar ƙalubalen sabuwar kakar wasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *