Wannan mataki, kamar yadda ƙudirin ya nuna, ya hada da “taƙaita tallafi ga Najeriya har sai an ɗauki matakai na gani da ido don kare al’ummomin Kirista da ke fama da tashe-tashen hankula na addini.”
Majalisar Wakilan Amurka ta gudanar da daftarin dokar kashe kuɗi na shekarar kuɗi, wanda ke ɗauke da tanadi na rage tallafin waje ga Najeriya saboda zargin nuna wariyar tashe-tashen hankula ga Kiristoci da sauran al’ummomin da ba su da kariya.
Wannan doka mai suna National Security, Department of State and Related Programs Appropriations Act na shekarar kuɗi ta 2027, Majalisar ta amince da ita a ranar Laraba da ƙuri’u 217 da suka goyi baya, sannan 209 suka ƙi.
Wannan ƙudiri ya ƙunshi tanadin janye dukkan tallafin waje ga Najeriya har sai Amurka ta tabbatar da cewa gwamnatin Najeriya tana ɗaukar matakan da suka dace don kare Kiristoci daga tashe-tashen hankula. Ƙudirin ya buƙaci “hukumta gwamnatocin ƙasashen waje da miyagun mutane da ke tsananta wa mutane saboda addininsu.”
- An saki ‘yan jarida biyu bayan shafe watanni a tsare a Nijar
- Rasha ta ayyana dokar ta ɓaci a yankin Crimea
- ‘Yan sanda sun kama masu garkuwa da masu bai wa ‘yan bindiga bayanai da masu safarar miyagun ƙwayoyi
Wannan mataki, kamar yadda ƙudirin ya nuna, ya haɗa da:“Taƙaita tallafi ga Najeriya har sai an ɗauki matakai na gani da ido don kare al’ummomin Kirista da ke fama da tashe-tashen hankula na addini.”
Haka kuma yana neman samar da “tallafi ga shirye-shiryen ‘yancin addini a ƙasashen waje da kuma kariyar ‘yancin addini ga ƙungiyoyin addini da ke rarraba tallafin waje.”
Dan majalisa Riley Moore da sauran wasu ‘yan jam’iyyar Republican, ciki har da Jeff Steube (mai wakiltar Florida), ne suka goyi bayan wannan tanadi.
An gabatar da kudirin ga Majalisar ne tun a watan Afrilu. Mr. Steube ya sanar da amincewa da kudirin a shafinsa na X (Twitter) inda ya ce:
Ya ce: “Kada masu biyan haraji na Amurka su taɓa tallafawa gwamnatocin da ke zuba ido ana yin garkuwa da Kiristoci, ana azabtar da su, kuma ana kashe su.”
Moore, wanda a baya ya zargi gwamnatin Najeriya da kisan kiyashi ga Kiristoci, ya matsa lamba don sanya jawabi a cikin dokar shekarar kuɗi ta 2027 don taƙaita tallafi ga Najeriya a kan hujjar cewa:Ya ce
Ya ce:”Ba a yi abubuwan da suka dace ba don yaƙar ‘yan ta’addan Fulani masu tsrajin Islama a yankin Tsakiyar Najeriya (Middle Belt).”
Dan majalisar na Republican ya shaida wa Majalisar cewa wannan tanadi yana ba da tallafi ga gwamnatin ne kawai idan aka samu ci gaba wajen kare al’ummar Kirista. Ya bayyana hakan a matsayin wani ɓangare na tsarin gwamnatin Trump na taimaka wa Najeriya wajen kare Kiristoci “yayin da ake tuhumar gwamnatin Shugaba Tinubu idan ta gaza.”
Ko da yake a farko kudirin ya taƙaita bayar da kashi 50 cikin ɗari (50%) na tallafin Amurka, Mr. Steube ya ba da shawarar janye dukkan tallafin waje baki ɗaya ga ƙasar.
[…] Majalisar wakilan Amurka ta ƙaddamar da dokar rage tallafin waje ga Najeriya […]