Shugabar Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF), Cathertsaro daussell, ta kai ziyara jihar Sokoto a ranar Juma’a domin duba halin da yara ke ciki a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya, inda rikice-rikicen tsaro da talauci da ƙarancin abinci ke ci gaba da jefa miliyoyin yara cikin buƙatar agajin gaggawa.
A yayin ziyarar, Russell ta gana da jami’an gwamnatin jihar tare da duba wasu shirye-shiryen da UNICEF ke tallafa wa domin inganta lafiyar iyaye mata da yara, tare da kare yara masu rauni.
Ta ce wajibi ne a tabbatar da cewa yara sun samu kariya duk da rikice-rikicen da ake fuskanta.
- Mummunan hatsarin ɗalibai: Gwamnatin Uganda ta hana makarantu fita yawon buɗe ido
- Akalla mutum 20 sun mutu a hare-haren ‘yan ta’adda a gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DRC)
- Majalisar wakilan Amurka ta ƙaddamar da dokar rage tallafin waje ga Najeriya
Arewacin Najeriya na ci gaba da fama da matsananciyar matsalar tsaro, wadda ta yi sanadin mutuwar dubban mutane.
Haka kuma, rikicin da ake ci gaba da fuskanta a Gabas ta Tsakiya ya ƙara tsananta matsalar ƙarancin abinci ga miliyoyin mutane masu fama da talauci, lamarin da ya sa yara daga iyalai marasa ƙarfi suka fi shiga cikin haɗari.
A cewar UNICEF, tsakanin miliyan 18.3 zuwa miliyan 23.4 na ƙarin yara daga gidajen da ke fama da matsanancin talauci a duniya sun ƙara shiga cikin mawuyacin hali, ciki har da tsakanin miliyan 6.5 zuwa miliyan 8.8 a nahiyar Afirka.
Najeriya na daga cikin ƙasashen duniya da ke da mafi yawan yara masu rayuwa cikin talauci, yayin da ƙungiyoyin agaji ke gargadin cewa yaran da ke yankunan da rikice-rikice suka addaba a arewacin ƙasar na daga cikin waɗanda suka fi buƙatar taimako.