Akalla mutane 20 ne suka mutu a cikin makon nan sakamakon hare-hare uku da ake zargin mayaƙan masu alaƙa da ƙungiyoyin jihadi ne suka kai a gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DRC), kamar yadda wani rahoto na RFI ya bayyana.
Hare-haren sun faru ne a yankin Beni da ke lardin North Kivu, tsakanin ranakun 12 zuwa 15 ga watan Yuli.
A ranar Lahadi, mayaƙan ƙungiyar Allied Democratic Forces (ADF), wadda ke da alaƙa da Islamic State (IS), sun kai hari a wani yanki da ke yammacin birnin Beni.
- Hare-haren Isra’ila a Gaza sun kashe aƙalla mutum 12
- Gobara ta hallaka aƙalla mutane 11 a Gidan marayu da ke Aljeriya
- Trump ya yi barazanar kai farmaki kan muhimman ababen more rayuwa na Iran
Birnin Beni shi ne hedikwatar gwamnatin lardin North Kivu tun bayan da ƙungiyar M23 ta ƙwace birnin Goma a bara.Harin ya yi sanadin mutuwar fararen hula bakwai, sannan sojoji uku na rundunar sojin Kongo sun faɗa tarkon kwanton bauna.
A daren Talata kuma, mayaƙan ADF sun kai hari garin Mangina, kusa da iyakar lardin Ituri, inda suka kashe fararen hula huɗu. A ranar Alhamis, wasu mutane goma sun sake rasa rayukansu a wani hari daban da aka kai a Mangina.
Mutanen da suka tsira daga hare-haren na ci gaba da tserewa zuwa tsakiyar garin Beni, wanda ya zuwa yanzu bai fuskanci hari ba. Ƙungiyar ADF ta shafe shekaru tana gudanar da munanan hare-hare a yankunan North Kivu da Ituri.
Laifukan da ake zarginta da aikatawa sun haɗa da satar mutane, tilasta wa mutane yin aiki ba tare da biyan su ba, ɗaukar yara aikin soja, tilasta aure da kuma tilasta wa mata ɗaukar ciki.
Wani sabon rahoto na Amnesty International ya zargi ƙungiyar da aikata laifukan yaƙi da kuma laifukan cin zarafin bil’adama.