Ƙungiyar Matan Jami’an ’Yan Sandan Najeriya (POWA) ta bai wa wasu mambobin ta kayan sana’o’i da na dogaro da kai, tare da wayar da kansu kan muhimmancin kula da lafiya, a wani ɓangare na ayyukan babban taronta na shekara ta 2026 da ake gudanarwa a Abuja

A taron da aka gudanar a Makarantar Sakandaren ’Yan Sandan da ke Abuja, shugabarƙungiyar POWA, Mutiat Disu, ta ce ƙungiyar za ta ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen da ke inganta lafiya da walwala da bunƙasa tattalin arzikin iyalan jami’an ’yan sanda ta hanyar shirin POWA CARES.

A cewarta, taron bana mai taken “Mace Mai Juriya: Fuskantar Kalubalen Rayuwa da Ƙarfi, Manufa da Kima”, ya nuna muhimmancin jajircewa da kuma kula da lafiya duk da ƙalubalen rayuwa.

Mutiat ta kuma gode wa abokan hulɗa da masu tallafa wa shirin bisa gudummawar da suka bayar wajen ganin an aiwatar da shirin.

A wajen taron, an raba kayan sana’o’i ga zaɓaɓɓun mambobi daga rassan POWA da ƙungiyoyin haɗin gwiwa.

Kayan sun haɗa da firiza da murhunan gas da keken ɗinki da injinan niƙa da kwamfutocin tafi-da-gidanka da injinan yin gurguru da dai sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *