Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Ondo ta kama wani mutum mai suna Amos Paul bisa zargin ƙona al’aurar ‘yarsa mai shekaru goma saboda  yin fitsarin kwance.

Lamarin ya faru ne a yankin Unaun, Upenme da ke ƙaramar hukumar Owo a jihar Ondo, inda aka ce mazauna yankin sun kai rahoton abin da ya faru ga ‘yan sanda, lamarin da ya kai ga cafke wanda ake zargin.

Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan  DSP Abayomi Jimoh, ya bayyana cewa yarinyar ta samu munanan raunukan ƙonewa a al’aurarta, kuma an garzaya da ita zuwa Asibitin Koyarwa na Tarayya (FMC),  inda likitoci ke ci gaba da ba ta kulawar gaggawa.

Jimoh ya ƙara da cewa an miƙa shari’ar zuwa Sashen Kula da Laifukan Mata da Yara (Gender Unit) na rundunar domin gudanar da cikakken bincike da kuma ɗaukar matakan doka da suka dace.

Jimoh ya tabbatar da cewa rundunar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen kare yara da sauran masu rauni daga cin zarafi, tashin hankali da kuma duk wani nau’in zalunci. Ya kuma jaddada cewa duk wanda bincike ya tabbatar da laifinsa zai fuskanci hukunci kamar yadda doka ta tanada.

Kwamishinan ya yi kira ga al’umma da su riƙa kai rahoton duk wani lamari na cin zarafin yara, rikicin cikin gida ko wasu laifuka masu kama da haka ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa, yana mai cewa haɗin kan jama’a na da muhimmiyar rawa wajen kare rayuka da haƙƙin yara.

Rundunar ta ce bincike kan lamarin na ci gaba, yayin da ake tsare da wanda ake zargin har zuwa kammala bincike da gurfanar da shi a gaban kotu idan an tabbatar da zargin.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *