A ranar Jumma’a za a fara taron kwana uku na horar da mata masu gudanar da harkokin ƙwallon ƙafa da Hukumar Ƙwallon ƙafa ta Duniya, FIFA, ta shirya a Abuja. 

Hakan na cikin shirin da Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Najeriya, NFF, ta ɗauka don karfafa jagoranci da gudanarwa a ɓangaren ƙwallon ƙafa ta mata a ƙasar.

Tuni dai aka kammala shirye-shiryen gudanar da taron yayin da ƙwararrun mata biyu daga FIFA wadanda za su jagoranci taron, wato Thubaelihle Sibanda da Tsholofelo Setlhoko suka riga suka iso.

Za su yi aiki tare da wasu ƙwararru daga Najeriya ciki har da mamba a kwamitin zartarwa na NFF kuma mamba a kwamitin yada labarai na FIFA, Aisha Falode, Farfesa Mariam Suleiman daga Jami’ar Ahmadu Bello, kwararriya a harkokin wasanni Dr Anthonia Uwa, da kuma jami’in koyar da alkalan wasa na FIFA, Mohammed Ameenu.

Jimillar mata 41 ne za su halarci wannan horo. Cikin su akwai jami’ai 20 daga Gasar Cin Kofi ta Mata ta Najeriya, NWFL, sakatarorin hukumomin ƙwallon ƙafa na jihohi 3 da suka haɗa da Lagos, Yobe da Nasarawa, da kuma ma’aikatan NFF 15.

Taron horarwar na daga cikin shirin Hukumar FIFA na ganin an ƙarfafa jagoranci, mulki da samar da ci gaba mai dorewa na ƙwallon ƙafa ta mata a ƙasashe da suke mambobinta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *