Shugaban ƙungiyar Atlético Madrid, Miguel Angel Gil, ya bayyana cewa ɗan wasan gaba Julián Álvarez ba zai bar ƙungiyar ba a wannan bazara ta hada haɗar ‘yan wasa.
Gil ya ce matsayinsa da na ƙungiyar a bayyane yake kuma tuni suka sanar da ɗan wasan da wakilan sa da kuma shugaban Barcelona da cewa ba sa son sayar da shi.
“Na yi imani cewa a yanzu Atlético ita ce ƙungiyar da tafi dacewa ga Julián, kuma shi ne ɗan wasan gaba da ya fi dacewa ga Atlético Madrid. Muna son ya zauna a nan,” in ji shi.
-
FIFA za ta bai wa tawagar da ta lashe Gasar Kofin Duniya ta 2026 zobe na zakaru a karon farko
-
Abin da ya kamata ku sani game da Alkalin Wasan Karshe na Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026
-
FIFA ta fara horas da masu tafiyar da harkokin ƙwallon ƙafa na mata a Abuja
A cewar shugaban na Atlético Madrid, ya ji cewa shugaban Barcelona ya ce suna da kuɗi mara iyaka da za su bayar domin siyan ɗan wasan.
Ya mayar da martini cewa Atlético ita ma tana da amsa mara iyaka”.
“Ba mu son mu sayar da shi. Ba mu amince da tayin Yuro miliyan 100 ba, ba za mu kuma amince da tayin Yuro miliyan 150 ko 200 ma ba,” in ji Gil.
Wannan na nufin Álvarez zai ci gaba da kasancewa a filin wasa na Wanda Metropolitano duk da raɗe-raɗin da ke haɗa shi da koma wa Barcelona.
