Wani mai haɗa wasan dambe, Dr Ezekiel Adamu, ya ce idan aka haɗa karambatta tsakanin Anthony Joshua da Moses Itauma a Najeriya, zai janyo idanun duniya fiye da fafatawar Muhammad Ali da George Foreman da aka yi masa laƙabi da ‘Rumble in the Jungle’ a Turance.
Dukka ‘yan wasan damben biyu na ƙasar Birtaniya suna da asali na Najeriya.
Joshu, wanda zai dawo fafatawa a wannan wata da Kristian Prenga, ana sa ran kuma zai fafata da abokin hamayyarsa Tyson Fury, yayin da Itauma kuma zai fafata da Filip Hrgovic a ranar 29 ga Agusta.
-
Atlético Madrid ta ce Julián Álvarez ba na sayarwa ba ne
-
Flying Eagles za ta fara kare kambun WAFU B akan Ghana
-
FIFA za ta bai wa tawagar da ta lashe Gasar Kofin Duniya ta 2026 zobe na zakaru a karon farko
“Wannan fafatawa ce ta duniya. Za mu samu ɗimbin masu kallo,” in ji Adamu a hirarsa da Sky Sports.
“Idan ka duba Afirka baki ɗaya, muna da mutane biliyan 1.4. Kashi 70 zuwa 75 na wannan al’umma suna tsakanin shekaru 15 zuwa 30. Idan suka kalli wannan fafatawa zai zama babban al’amari”.
“Dukkaninsu taurarin duniya ne. Don haka labari ne mai cikakken tarihi ga Afirka, inda suka fito daga tushe guda”.
“Wannan ita ce fafatawar da za ta zarce ‘Rumble in the Jungle’ da mu ke magana akan ta tsawon shekaru 50. Ina so mu gudanar da wannan fafatawar a nan.”
